BBC navigation

Gaza: Isra'ila ta jingine shirin kai hari ta kasa

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 09:00 GMT

Hayaki ya turnuke sararin samaniyar Gaza sakamako hare-haren Isra'ila

Rahotanni daga Isra'ila sun ce gwamnatin kasar ta dakatarda shirinta na kai wa zirin Gaza hari ta kasa, yayin da ake ci gaba da tattaunawar dakatar da bude wuta da Masar ta gabatar.

Majalisar zartarwar Israilan da kwashe daren Litinin tana wani taro domin tattauna makomar farmakin sojin da ta kwashe mako daya ta na kaiwa kan zirin Gaza.

Sai dai kuma an kwana ana gwabza fada a zirin na Gaza in da rahotanni suka ce an kai sababbin hare-haren bom da kuma na rokoki, a daidai lokacin da rikicin ya bazu zuwa wasu sassan gabar Yammacin Kogin Jordan.

Majiyoyi a Gazan sun ce wani hari ta sama da Israila ta kai ya kashe iyali daya mai mutum hudu a kauyen Bait Lahiya, yayinda su kuma mayakan Falasdinawa suka harba rokoki fiye da dari daya zuwa cikin Israila tsakanin ranakun Litinin da Talata.

Kokarin shiga tsakani

Har yanzu dai ba a san irin sharuddan da shirin kawo zaman lafiya da Masar ke son fitowa da shi ya kunsa ba.

Sai dai Israila da Hamas sun bayar da nasu sharuddan da suke son a shigar cikin shirin na kawo zaman lafiya.

Sharuddan da Isra'ila ta gindaya dai sun hada da dakatar da harba makami kowane iri zuwa cikin yankunan ta kuma kasashen duniya su hana Hamas sake samun makamai.

Yayin da Hamas ta ce dole ne a kawo karshen killacewar da aka yiwa Gaza kuma Isra'ila ta kawo karshen abin da ta kira kisan gillar da take yiwa Falasdinawa.

A yanzu dai babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban-ki-Moon ya isa birnin Alkhahira na Masar domin taimakwa wajen cimma sulhu, kuma yana shirin ganawa da Farayin Ministan Israila Benjamin Natanyahu da kuma shugaban Falasdinawa Mahmood Abbas a cikin kwanakki masu zuwa.

Ya zuwa yanzu dai hare-haren na Israila sun hallaka falasdinawa 105 a cikin kwanaki bakwai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.