BBC navigation

'Ba mu a cikin hadakar 'yan adawar Syria'

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 09:03 GMT

Wasu 'yan tawayen Syria masu kishin Islama a sansanin karbar horo

Kungiyoyin 'yan tawaye masu kaifin kishin Islama a birnin Alleppo na kasar Syria sun ce ba su amince da kungiyar nan ta gamayyar kungiyoyin 'yan adawar Syria wadda kasashen Yamma ke marawa baya ba.

A cikin wani faifan bidiyo da suka sa a shafin internet, sun yi fatali da abin da suka kira wani ''shiri na hadin baki'', kuma suka ce su suna son kafa kasa mai bin tsarin addinin Islama ne.

Wannan dai ya zo ne a ranar da Tarayyar Turai ta amince da sabuwar kungiyar a zaman halattaciyar wakiliyar mutanen Syria.

A cikin faifan bidiyon, an nuno wani mai magana da ba a shaida shi ba gaban wani dogon teburi tare da wasu mutane akalla ashirin, gaban wata tuta baka;inda ya karanto sunayen wasu kungiyoyin 'yan tawaye masu kishin Islama goma sha uku wadanda suka yi watsi da kafa hadakar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.