BBC navigation

''Tallafin Ilmin Burtaniya bai yi tasiri ba a Najeriya''

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 09:12 GMT

Yarinya 'yar makaranta a Najeriya

Wani bincike da wata kungiya mai sanya ido kan tasirin tallafin kasa da kasa ta gudanar ya nuna cewa miliyoyin fam-fam na ingila da gwamnatin Birtaniya ta ke baiwa makarantun Najeriya tallafi bai kawo kowanne irin chanji a karantun yaran Najeriyar ba.

Kungiyar mai suna Independent Commission for Aid Impact ta ce karancin kwararrun malamai da kuma rashin goyon baya daga hukumomin Najeriyar ne suka yi wa kokarin na Burtaniya zagon kasa.

Ya zuwa yanzu dai Fam miliyan dari da biyu ne Birtaniya ta kashe wajen tallafawa ilmi a jahohi goma na Najeriya tare alkawalin kashe wasu fam miliyan dari da ashirin da shidda daga nan zuwa shekara ta 2019.

Sai dai kungiyar ta ce bitar da suka yi kan tasirin wadannan kudaden da aka kashe ta nuna cewar babu wani tasirin a zo a gani da kashe kudin yayi waje kyautata koyon karatu ga yaran Najeriya.

'' Dan takaitaccen bincike''

Tace shirin tallafawa ilmi na hukumar raya kasashen ta Burtaniya DFID wanda a karkashin sa ne ake kashe kudaden ana aiwatar da shi a cikin yanayi mai cike da kalubale da ya hada da kwararrun malamai 'yan kadan, da rashin azuzuwa wadatattu da kuma rashin tabbas a yanayin samarda kudade daga gwamnatin kasar.

Rahoton kungiyar ya ce ya gano cewar kashi daya bisa uku na yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta su kimanin miliyan uku da dubu 700 har yanzu ba su makarantu, yayinda wadanda suka shiga makarantun ba su gane wani abu ba.

Sai dai mai magana da yawun hukumar ta DFID ya mayar da martani da cewar binciken takaitacce ne domin tawagar kungiyar ta ziyarci kashi daya cikin dari ne na makarantun da hukumar ke tallafawa kuma kusan dukkansu a jaha daya a Najeriyar suke alhali hukumar na aiki ne a jahohi goma.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.