BBC navigation

Cocin Anglican ya ki amincewa da nada mata limamai

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:39 GMT

Sarauniyar Ingila ta na gaisawa da babban limamin cocin Anglican

Cocin Anglican ya ki amincewa da shirin nada mata a matsayin Bishop-bishop, wato limamai, matakin da ya kawo karshen shekaru 12 na kokarin yin doka akai.

Kadan ya rage dai kudurin ya kasa samun amincewar kashi biyu bisa uku na goyon bayan hukumar gudanarwar cocin .

Babban limamin cocin Ingilan mai barin gado, Archbishop na Canterbury Rowan Williams, ya ce shi kansa bai ji dadin yadda sakamakon ya kasance haka ba.

Masu adawa da shirin dai sun ce babu wani wuri da littafin addininsu ya ba da damar nada mace a wannan mukami na bishop.

Ranar Bakin Ciki

Shi ma Arch Bishop na Cantebury mai jiran gado Justin Welby, ya fada a shafin internet na twitter cewa wannan rana ce ta bakin ciki.

Sai dai yayin da a Ingilan hakan ta kasance, ita kuwa matar da aka nada a matsayin Bishop din a kasar Swaziland Ellinah Wamukoya kira ta yi ga cocin na Ingila.

Tace ''ina son yin kira ga cocin Ingila yau da su daina duba jinsin mutane su rinka nada mutane bisa gudummawar da zasu baiwa cocin ba tare da la'akari da jinsinsu ba''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.