BBC navigation

Falasdinawa sun bindige 'yan uwansu shida

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:48 GMT

Mayakan kungiyar Hamas

Wasu 'yan bindiga rufe da fuskoki sun harbe wasu falasdinawa shida da suke zargi da yiwa Isra'ila leke asiri a birnin Gaza.

Wani dan jarida da ke can ya shaidawa bbc cewar ya ga lokacinda aka daura gawar daya daga cikinsu ga babur ana janta a kan titi a ranar talata.

Jami'an Isra'ila dai sun ce sun dogara ne kan wasu falasdinawa 'yan leken asiri da suka baza a cikin birnin na Gaza domin taimaka musu gane inda suke son kai ma hari.

Amma Hamas ba ta bayarda wata shaida ba dake nuna mutanen 'yan leken asiri ne ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.