BBC navigation

An kai harin bam a Tel Aviv

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:14 GMT

Mutane akalla 20 ne suka ji rauni, biyu daga ciki munana, a wani harin bam da aka kai cikin wata motar bus a birnin Tel Aviv.

Hotunan talabijin sun nuna motar bus din tsaye kusa da hedkwatar ma'aikatar tsaron Isra'ila, tagoginta a farfashe kuma hayaki na fitowa daga cikinta.

An kwashe galibin wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti dake kusa.

Wani likita, Parfesa Pinchas Halpern, ya ce: "Ya zuwa yanzu mun karbi mutane 21, daya daga cikinsu na cikin mawuyacin hali, daya kuma yana jin jiki ba sosai ba".

'Yan sanda na ci gaba da farautar wasu mutane biyu da ake zargin su su ka dasa bam din.

Kungiyar Hamas ta amsa cewar ita ta kai harin, kuma wakilin BBC a Gaza ya ce an yi ta harba bindigogi sama domin murnar jin labarin kai harin.

Hakan na zuwa ne bayan daren da aka kwashe dakarun Isra'ila na kai munana hare-hare ta sama a Gaza, yayin da ake kokarin diplomasiyya na cim ma tsagaita wuta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.