BBC navigation

An samu tashin hankali a jihohin Kano da Nasarawa

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:18 GMT
Kano

Kano ce jiha mafi yawan jama'a a Najeriya

An samu tashin hankali da ya haddasa asarar rayuka a karamar hukumar Bichi dake jihar Kano da kuma wasu sassan jihar Nasarawa dukkansu a arewacin Najeriya.

Wakilin BBC a birnin Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya ce rikicin ya barke ne bayan wani Kirista ya shiga kasuwa da wata riga mai dauke da kalaman da wasu ke ganin na batanci ne ga Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Wadansu mazauna garin su bayyana cewa an yi kone-kone, kuma an kashe akalla mutane hudu.

Sai dai wakilin na mu, yace jami’an tsaro a jihar sun ce babu wanda ya rasa ransa a tashin hankalin.

Hukumomi a jihar Nasarawa ta Nijeriya sun yi karin haske kan ta'adin da aka yi a mummunar rigima mai nasaba da kabilanci da ya aka yi tsakanin 'yan kabilar Eggon da 'yan kabilar Migili ko kuma Koro, a garin Agyaragu inda suka ce mutane goma sha biyu ne suka rasa rayukansu wasu fiye da haka kuma suka jikkata baya ga gidaje masu yawan gaske da aka kona.

Kawo yanzu dai tashin hankalin ya lafa, yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da sintiri a sassa daban-daban na yankin domin hana bazuwar rikicin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.