BBC navigation

An bada sammacin uwargidan tsohon shugaban Ivory Coast

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:23 GMT

Simone Gbagbo, uwargidan tsohon shugaban Ivory Coast

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta bada bada sammacin kama uwargidan tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Samoone Gbagbo, dangane da aikata muggan laifukan keta hakkin bil'adama a lokacin rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar.

Takaddar sammancin ta yi zargin cewa ita ke da alhakin kashe kashe, da yiwa mata fyade, da cin zarafin mutane da tursasawa jama'a da dai sauransu.

Wakiliyar BBC ta ce wasu masu sharhi sun ce Samoone Gbagbo ita ce ta yi- ruwa- ta yi tsaki wajan hana mai gidanta barin mulki.

Tuni dama mai gidanta Laurent Gbagbo ya ke Hague din inda yake fuskantar tuhumce tuhumcen aikata muggan laifuka kan biladama.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.