BBC navigation

Sarkozy zai gurfana a gaban kotu

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 09:48 GMT

Nicolas Sarkozy, tsohon shugaban kasar Faransa

Tsohon Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy, zai bayyana a gaban kotu a birnin Bordeaux na kasar ranar Alhamis, domin amsa tambayoyi kan alakarsa da matar da tafi arziki a Faransa Liliane Bettencourt.

Ana dai zargin Mista Sarkozy da karbar kudaden da suka saba ka'ida a matsayin tallafi ga jam'iyyarsa domin gudanar da yakin neman zabensa a shekara ta 2007, zargin da tsohon shugaban ya sha musantawa.

Tuni dai tsohon ma'ajin kwamitin yakin neman zaben tsohon shugaban ya ke fuskantar bincike kan wasu kudade da a ka bayar da suka saba ka'ida a wancan lokacin.

Dokokin Faransa dai sun kayyade yawan kudin tallafin da za a iya baiwa jam'iyyu; inda mutum daya ke iya bayar da dala dubu tara da dari biyar kawai a shekara daya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.