BBC navigation

An dakatar da kwamandan rundunar sojin Congo

An sabunta: 23 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:23 GMT

Sojojin Congo a garin Goma

An dakatar da kwamandan rundunar sojin Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango har sai an kammala binciken zargin cewar ya saidawa kungiyoyin 'yan tawaye da makamai.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ne ya zargi Janar Gabriel Amisi da gudanar da wani gungun masu samarda makamai da masu farautar giwaye da kuma kungiyoyin 'yan tawaye.

Wani kakakin gwamnatin kasar ya ce hakama ana binciken wasu jami'an sojin.

Dakatarwar ta biyo ne bayan kama birni Goma da 'yan tawayen M23 suka yi ranar Talatat da ta gabata.

T

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.