BBC navigation

'Yan adawa sun kira zanga-zanga a Masar

An sabunta: 23 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 11:23 GMT

Shugaba Muhammad Mursi na kasar Masar

Kungiyoyin 'yan adawa a Masar sun yi kira ga 'yan kasar da su fito domin wata gagarumar zanga-zanga ranar juma'a domin nuna rashin amincewa da wata dokar da Shugaba Muhammad Mursi ya kafa wadda ta bashi karin iko.

'Yan adawar dai sun bayyana matakin a zaman yiwa halattacen tsarin doka juyin mulki, sannan kuma suka zargi shugaban da nada kansa a zaman wani sabon Fira'una.

Sabuwar dokar dai ta tanadi cewar babu hukumar da ke da karfin soke duk wani hukumcin da shugaban kasa ya zartar ciki kuwa har da kotu.

Sai dai magoya bayansa sun ce an fito da sabon tsarin ne domin kare juyin juye halin kasar kuma jim kadan bayan sanarda dokar, dubban magoya bayan nasa suka yi ta shagalin murnar kafa ta gaban ginin Babbar Kotun Kasar dake birnin Alkhahira.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.