BBC navigation

Isra'ial ta kashe wani Bafaladtsine a Gaza

An sabunta: 23 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:07 GMT
Isra'ial ta kashe wani Bafaladtsine a Gaza

An kashe mutumin ne a kan iyakar Isra'ila da Gaza

Rahotanni daga Zirin Gaza sun ce wani Bafaladtsine guda ya rasa ransa bayan da sojojin Isra'ila suka bude masa wuta a kusa da garin Khan Yunis.

An kuma raunata wasu karin Falasdinawan goma.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta yi harbin gargadi bayan da wasu gungun mutane suka nufi kan iyakarta da Gaza.

Wadanda suka shaida lamarin sun bayyana mutanen da cewa manoma ne.

Mutumin dai shi ne na farko da ya rasa ransa tun bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla ranar Laraba wacce ta kawo karshen fadan da bangarorin biyu suka shafe kwanaki takwas suna yi.

Tun da farko Isra'ila ta ce ta kama wasu mutane da dama wadanda take zargin suna da hannu a harin bam din da aka kai birnin Tel Aviv ranar Laraba.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce wani mutum dan shekaru 20 Anwar Qdeih, ya rasa ransa, sannan wasu karin goma suka samu raunuka.

Dangin Mr Qdeih, sun ce yayi kokarin sanya tutar Hamas ne a kan iyakar, lokacin da sojojin Isra'ila suka bude masa wuta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.