BBC navigation

An kama mutun daya dangane da kai hari a Tel Aviv

An sabunta: 23 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:51 GMT

Motar bus din da aka kaiwa harin bom

Hukumomi a Isra'ila sun kama wani balaraben Isra'ilan wanda suke zargi da laifin kai harin bam din da ya tashi a wata motar safa a birnin Tel Aviv ranar Laraba.

Mutane 29 ne suka samu raunuka a harin, wanda aka kai sa'oi kadan kafin fara aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin Isra'ila da Hamas, wadda ta kawo karshen kwanaki 8 na tashin hankali a Gaza.

Harin wanda aka kai a lokacin da jama'a ke cincirindo shi ne na farko a irinsa birnin na Tel Aviv cikin shekaru 6.

Yanzu dai mazauna zirin Gaza da na kudancin Isra'ila sun kwashe rana ta farko cikin kwanciyar hankali ciki sama da mako daya yayin da yarjejeniyar dakatar da bude wutar ke cigaba da kankama.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.