BBC navigation

Saliyo: an kidaya mafi yawan kuri'u

An sabunta: 23 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:06 GMT

Tutar Saliyo

Yanzu haka dai an kidaya kashi casa'in daga cikin dari na kuru'un da aka kada a zaben shugaban kasar da aka yi a Saliyo a karshen makon da ya gabata.

Sai dai har yanzu ana cigaba da tantance ragowar kuru'un, sakamakon wasu zarge-zargen magudi da 'yan adawa suka yi.

Wannan dai shi ne zaben farko da Saliyon ta shirya da kanta, tun bayan karshen yakin basasa a kasar shekaru 10 da suka wuce. Zabubuka 2 da aka yi a baya, majalisar dinkin duniya ce ta shirya su.

Kasar ta Saliyo dai tayi fama da mummunan yakin basasa a baya, inda aka yi asarar rayuka da dama.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.