BBC navigation

Mutane 11 ne suka rasu a harin bam na Jaji

An sabunta: 25 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:17 GMT
Hari kan Coci a Kaduna

Hari kan Coci a Kaduna

Rundunar sojan Najeriya tace, an kai harin bam na kunar bakin wake har ribi biyu a wani coci dake cikin harabar barikin soja dake Jaji, a kusa da garin Kaduna.

Alkaluma na nuna cewa mutane goma sha daya ne suka mutu, yayin da wasu mutanen kusan talatin suka jikkata.

Harin farko dai wani ne ya aukawa cocin da mota kirar bus dake makare da bam, yayin da mabiya addinin Krista ke addu'oi.

Minti goma bayan faruwar hakan kuma sai wani bam din daban da aka sanya acikin wata karamar mota ya tashi.

Wakilin BBC yace kakakin sojan Najeriyar yace, an ga gawarwakin wadanda bam din ya hallaka, sai dai kuma har yanzu ba a tantance yawan wadanda harin ya hallaka ba.

Rundunar sojan Najeriyar dai ta bakin kakakinta ta zargi kungiyar Boko Haram da kai harin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.