BBC navigation

Hari a Abuja: 'Yan sanda sun yi kame

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:17 GMT
Abuja

Wannan ne hari na baya-bayan nan da ake kaiwa a Najeriya

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba, sun kai hari kan wani ofishin 'yan sanda a Abuja babban birnin Najeriya, inda ake ajiye 'ya'yan kungiyar Boko Haram da aka kama.

Wani mai magana da yawun 'yan sanda ya ce sun mayar da martani ga harin.

Sanarwar da rundunar 'yan sandan ta fitar, ta ce jami'anta biyu sun mutu a harin, yayin da ta kame biyu daga cikin maharan.

Rundunar ta ce mutane 30 ne daga cikin wadanda ake tsare da su a wurin suka tsere, amma ta ce ta sake kame 25 daga ciki, yayin da ake ci gaba da neman ragowar biyar.

Kaddamar da bincike

Sufeto Janar na 'yan sanda MD Abubakar, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda ya umarci a gudanar da bincike kan yadda lamarin ya faru, sannan ya nemi a kara tsaurara matakan tsaro a gine-ginen gwamnati da kuma na 'yan sanda a kasar.

Hedkwatar hukumar tsaro ta musamman da ke kula da 'yan fashi da makami, na kusa da gine-ginen gwamnati, kuma ana tsaurara matakan tsaro a wurin.

Babu dai wata kungiyar da ta dauki alhakin wannan hari kawo yanzu.

Amma kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare makamantan wadannan a baya, inda ta kashe daruruwan mutane a bana, mafi yawanci a Arewacin kasar.

Harin na zuwa ne kwana guda bayan da wasu tagwayen harin kunar bakin wake suka kashe mutane 11 a wata majami'a da ke barikin soji a jihar Kaduna.

Wani mazaunin Abuja ya ce yaji karar harbe-harben da aka shafe kusan minti 30 ana yi da sanyin safiyar ranar Litinin.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ce babu wata alama ta barna da aka yi wa ginin, wanda ake baiwa tsaro matuka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.