BBC navigation

An kashe 'yan sanda biyu a harin Abuja

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:02 GMT

'Yan sandan Najeriya na fuskantar hare-hare a 'yan shekarun nan

Akalla 'yan sanda biyu ne suka mutu a wani hari da wasu 'gungun 'yan bindiga' suka kai kan wani babban ofishin 'yan sanda a Abuja - Najeriya, abinda ya sanya wasu da ake zargi da aikata fashi da makami guda biyar suka tsere.

Sanarwar da rundunar 'yan sandan ta fitar, ta ce ta kame biyu daga cikin maharan.

Rundunar ta ce mutane talatin ne daga cikin waɗanda ake tsare da su a wurin suka tsere, amma ta ce ta sake kame 25 daga ciki, yayin da ake ci gaba da neman ragowar biyar.

Ƙaddamar da bincike

Sufeto Janar na 'yan sanda MD Abubakar, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda ya umarci a gudanar da bincike kan yadda lamarin ya faru, sannan ya nemi a kara tsaurara matakan tsaro a gine-ginen gwamnati da kuma na 'yan sanda a kasar.

Hedkwatar hukumar tsaro ta musamman da ke kula da 'yan fashi da makami, na kusa da gine-ginen gwamnati, kuma ana tsaurara matakan tsaro a wurin.

Babu dai wata ƙungiyar da ta ɗauki alhakin wannan hari kawo yanzu.

Amma ƙungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare makamantan waɗannan a baya, inda ta kashe ɗaruruwan mutane a bana, mafi yawanci a Arewacin ƙasar.

Harin na zuwa ne kwana guda bayan da wasu tagwayen harin kunar bakin wake suka kashe mutane goma sha ɗaya a wata majami'a da ke barikin soji a jihar Kaduna.

Wani mazaunin Abuja ya ce yaji ƙarar harbe-harben da aka shafe kusan minti 30 ana yi da sanyin safiyar ranar Litinin.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ce babu wata alama ta ɓarna da aka yi wa ginin, wanda ake baiwa tsaro matuƙa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.