BBC navigation

An naɗa ɗan Canada gwamnan bankin Ingila

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:36 GMT

An naɗa shugaban babban bankin ƙasar Canada a matsayin sabon gwamnan Babban Bankin Ingila.

Mark Carney, ɗan ƙasar ta Canada, zai karɓi muƙamin da ake yi ma kallon ɗaya daga cikin mafiya muhimmanci a Birtaniya ne daga hannun Sir Mervyn King cikin watan Yulin baɗi.

A kawanakin baya ne aka ƙara ma Babban Bankin na Ingila ƙarfi, domin ya riƙa sa ido kan ayyukan cibiyoyin kuɗi, baya ga aikinsa na ƙayyade kuɗin ruwa.

Yayin da Birtaniya har yanzu ke cikin matsalar tattalin arzikin ƙasa da dama na kallon Mr Carney a matsayin wanda zai iya farfaɗo da tattalin arzikinta.

Shi ne zai kasance ɗan ƙasar waje na farko da zai riƙe muƙamin tun baya kafa bankin sama da shekaru 300 da suka wuce.

Ministan kuɗin Birtaniyar, George Osborne, yace Mark Carney ne mutumen da yafi dacewa ya zama gwamnan Babban Bankin Ingilan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.