Kwalejin aikin jaridar BBC ta ƙaddamar da ƙarin harsuna

BBC
Image caption Waɗannan shafuka na bai wa miliyoyin 'yan jarida damar ganin salon aikin jarida na BBC

Kwalejin Aikin Jarida ta BBC ta ƙaddamar da sabbin dandalin intanet guda huɗu: Hausa, da Sinanci mai Sauƙi, da Sinancin Gargajiya da kuma Urdu.

Duka sun maida hankali ne a kan rashin nuna bambanci, da rashin kuskure wajen amfani da harshen da ake watsa labaran da shi da kuma akidojin aikin jarida na BBC.

Yayin da ake da masu gabatarwa da mashirya shiri da ke aiki a sassan harsuna daban-daban na BBC suna watsa shiri a cikin harsunansu, hakan ta sanya shafukan intanet na Kwalejin Aikin Jarida suna ta ƙara zama wani rumbun ilimin dukkan sassa, wanda ke taimaka wa 'yan jaridar BBC da ke London da ma ƙasashen waje.

Za ku iya shiga cikakken sabon shafin kwalejin ta hanyar latsa nan

Sabon shafin Hausa

Sabon dandalin Hausa na Kwalejin Aikin Jarida ya wallafa cikakken jagora a kan ƙa'idar rubutun Hausa da nahawun Hausar.

Yayin da muke aiki a kan dandalin sai muka ga cewa don yin amfani da haruffan da suka dace, ana buƙatar samar da haruffan nan masu lanƙwasa, wato ɓ, da ɗ da ƙ, waɗanda ke cikin abcd na Hausa. In ba da su ɗin ba, akan sami rikici wajen bambance kalmomin da ke kama da juna, waɗanda guda ke da harafi ko haruffa masu lanƙwasa guda kuma babu.

Mun yi magana da Sashen Hausa muka fahimci cewa sun daɗe suna begen samun haruffan da za su raba waɗanda ke da lanƙwasa da waɗanda ba su da ita.

Don bambance haruffa masu lanƙwasa da waɗanda ba su da su, wasu kan yi amfani da baƙin ɓoye a kan kowane harafi mai lanƙwasar. Sam kuwa, ba zai yiwu mu wallafa dandali ba wanda ke koyar da yadda ake rubutu ba tare da haruffan da suke daidai ba.

Don haka, sai muka shiga neman haruffan da suka dacen, kuma ko shakka babu, da muka same sun, mun bai wa su ma Sashen Hausa.

Haka kuma dandalin na Hausa yana da bayanai a kan ƙa'idojin BBC wajen amfani da kafofin sada zumunta, haɗe da sauran ƙa'idojin aiki irin su rashin nuna bambanci, da 'yanci, da aiki ba kuskure da kuma riƙon amanar jama'a.

Waɗannan shafuka na kyauta suna kuma bai wa miliyoyin 'yan jarida a duk faɗin duniya damar ganin salon aikin jarida na BBC.