BBC navigation

Congo ta ce M23 sai ta janye daga Goma kafin tattaunawa

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:26 GMT

Shugaban Congo Joseph Kabila

Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta ce ba za ta yi wasu shawarwarin sasantawa da kungiyar tawaye ta M23 ba har sai ta janye daga birnin Goma wanda ta kwace a makon da ya gabata.

Sanarwar ta zo ne kwana daya bayan taron koli na kasashen Afrika da aka yi a kasar Uganda wanda ya nemi 'yan tawayen su janye daga Goma.

Wani kakakin 'yan tawayen, ya ce, duk wata janyewa da za su yi daga Goma za ta biyo bayan sakamakon tattaunawar sulhun ne, ba ta zamo wani sharadi ba.

Shugaban kasar Congon Joseph Kabila, ya gana da wakilan 'yan tawayen a birnin Kampala na Uganda a ranar Asabar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.