BBC navigation

An gaza cimma daidaito kan shugabancin Jami'yyar adawa a Faransa

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:20 GMT

Jean Francois Cope da Francois Fillon

Wani yunkuri da aka yi na warware takaddama mai zafi dangane da makomar Shugabancin babbar Jam'iyyar adawa ta masu ra'ayin rikau ta Faransa ya ci tura.

Bayan Jam'iyyar ta UMP ta yi zabe na cikin gida a makon da ya gabata, 'yan takara biyu sun zargi juna da laifin aringizon kuri'u.

Jean Francois Cope shine aka yi shelar ya samu nasara, to amma tsohon Prime Minista Francois Fillon ya nemi a sake kidaya kuri'un.

Shiga tsakanin da wani tsohon Prime Minista Allaine Juppe ya yi ya ci tura.

Sai dai wakilin BBC a birnin Paris ya ce, a yanzu lokacin mutuwar Jam'iyyar ta UMP kawai ake jira.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.