BBC navigation

Shugaban Masar Morsi na neman a sasanta

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:09 GMT

Shugaban Masar Mohammed Mursi

Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi ya fara neman sasantawa da masu adawa da shi a wata jayayya mai zafi a kan jerin ikon da ya baiwa kansa.

Mr Morsi ya ce shawarar da ya yanke a makon da ya gabata ta baiwa kansa ikon da babu wanda zai iya kalubalantar sa, ta wani dan lokaci ce.

Ya ce "a shirye yake ya bayar da hadin kai a sasanta a kan daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Shugaba Morsi zai gana da manyan Alkalan kasar a yau Litinin a kokarin yayyafa ruwa ga kurar da ta taso.

Jerin ikon da ya baiwa kansa ya haddasa zanga-zanga mai muni a duk fadin kasar da kuma karyewar darajar hannayen jari a kasuwar hada-hadar hannun jari ta Masar.

Masu fafutuka a zanga-zangar da ake yi a dandalin Tahrir wadanda suka hada da Nagy Soliman na Free Egyptian Party sun ce 'yan adawa ba za su ba da kai bori ya hau ba, har sai Mr Morsi ya canza shawara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.