BBC navigation

Shugaba Morsi ya gana da alƙalan Masar

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:24 GMT
Masar

Sabuwar dokar ta haifar da zanga-zanga da kone-kone a kasar

A wani yunkuri na yayyafa ruwa a kurar da ke neman turnuke harkokoin siyasar Masar, shugaba Muhammad Morsi ya gana da manyan alƙalan ƙasar a ƙoƙarin da yake na shawo kan rikicin siyasar da ya biyo bayan ƙudurin da ya fadada ikonsa.

Taron na zuwa ne gabanin wata zanga-zanga da aka shirya ranar Talata, ta magoya baya da kuma masu adawa da shugaban kasar mai ra'ayin musulunci.

Ofishin shugaba Morsi dai na cewa dokar ta wucin gadi ce, amma ta haddasa dauki-ba-dadi, da ma yajin aiki na masu adawa da shugaban kasar a wasu sassa na kasar ta Masar.

Tun da farko shugaban kasar ya ce yana fatan cimma matsaya da sauran masu ruwa da tsaki a kasar.

Ya kara da cewa yana son kuma cimma daidaito kan sabon kundin tsarin mulkin da ake rubuta wa yanzu haka, sannan ya ce sabuwar dokar na da nufin kare turakun demokuradiyya ne kawai.

Muna Makram Ebeid wata 'yar adawa ce a Masar din tana kuma fatan a cimma matsaya.

"Sassaucin na iya kasancewa, watakila ya cire wasu daga cikin batutuwan dake janyo kace-nace a tsarin mulki, wadanda suka saba doka".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.