BBC navigation

An buɗe babban taro kan matsalolin ɓangaren shari'a a Nijar

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:35 GMT
Shugaba Mahammadou Issoufu na Nijar

Za a tattauna matsalolin shari'ah a Nijar

A jamhuriyar Nijar yau ne Shugaban ƙasar Alhaji Issoufou Mahamadou ya jagoranci bikin buɗe wani babban taro na ƙasa baki- ɗaya, wanda zai duba matsalolin da hukumomin Shari'a na ƙasar ke fuskanta

Taron wanda shi ne irinsa na farko da aka taɓa shiryawa a fannin shari'a a kasar, ya haɗa wakilai kusan 500

A ƙarshe kuma ana son ya bayar da shawarwari a kan yadda za a warware duk wasu matsalolin da ke hana ruwa gudu a harkar shari' a ƙasar

Matsalar cin hanci da rashawa da rashin isassun Alƙalai da rashin kayan aiki na wasu daga cikin irin matsalolin dake addabar ɓangaren shari’ar ƙasar.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.