BBC navigation

Ana gagarumar zanga-zangar adawa a Masar

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:00 GMT
Zanga Zangar 'yan adawa a Alƙahira

'Yan adawa a Masar sun gudanar da zanga zanga

Dubban Misarawa ne suka cika maƙil a dandalin Tahrir a birnin Alƙahira, domin nuna fushinsu kan ƙarfin ikon da shugaban ƙasar na jam'iyyar 'yan uwa musulmi, Mohammed Morsi ya baiwa kansa.

A duk tsawon yau ɗin nan masu zanga-zangar na ta kwarara zuwa dandalin, su na yin maci daban-daban kuma suna rera waƙoƙin ƙin jinin shugaban ƙasar da kuma jam'iyyar 'yan uwa musulmai.

An soke wata zanga-zangar magoya bayan Shugaba Morsi domin gudun samun ƙarin rikici.

Shugaba Morsi ya yi ƙoƙarin yayyafawa wutar rikicin ruwa, inda ya yi alƙawarin taƙaita sabbin ikon da ya baiwa kansa.

Sai dai kuma masu zanga-zangar na neman ya janye su ne baki ɗaya.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.