BBC navigation

An kori shugabar Hukumar BPE a Najeriya

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:19 GMT
Goodluck Jonathan

Ana samun matsala a yunkurin sayar da fannin wutar lantarki na kasar

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sallami shugabar hukumar sayar da kadadorin gwamnati Bolanle Onogoruwa daga aiki ba tare da bayar da wani dalili ba, a daidai lokacin da ake shirin sayar da fannin wutar lantarki.

A baya dai majalisar dattawan kasar ta bayar da shawarar sauke ta daga aiki saboda, a cewarta binciken da ta yi a fannin sayar da kadarorin gwamnatin kasar ya samu Ms Onagoruwa da aikata ba daidai ba.

Wata sanarwa da ofishin mataimakin shugaban Najeriya, Mohammed Namadi Sambo, ya fitar ta tabbatar da sauke Ms Bolanle Onagoruwa daga shugabancin hukumar, koda yake ba ta fadi dalinlin sauke ta ba.

Sanarwar mai sakin layi biyu, ta kara da cewa sallamar za ta fara aiki ne nan take; kuma za ta mika duk wadansu hidimomin ofishinta ga Mr Benjamin Ezra, darakta mafi girman mukami a hukumar, wanda zai yi rikon shugabancin hukumar.

'Karo da juna'

Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kadan bayan da aka samu bayanai masu karo da juna tsakanin shugaba Jonathan da kakakinsa game da dakatar da mika wata cibiyar rarraba wutar lantarki ga kamfanin Manitoba na kasar Canada.

A ranar 14 ga watan Nuwamba ne kakakin shugaban kasar, Rueben Abati ya shaida wa manema labarai cewa an soke kwangilar da aka bai wa kamfanin Manitoba saboda ba a bi ka'ida wajen bayar da ita ba.

Kwanaki kadan bayan hakan shugaba Jonathan ya ce kwangilar na nan ba a soke ta ba.

Wannan dai shi ne karo na biyu da wani babban jami'in gwamnatin ke barin mukaminsa game da sayar da kadadorin gwamnatin a watannin baya bayan nan.

Tsohon minsitan samar da hasken wutar lantarkin kasar, Farfesa Barth Nnaji ma ya sauka daga mukaminsa a watan Agustan da ya gabata, bayan da aka gano cewa kamfaninsa na daga cikin wadanda ke yunkurin sayen wani kamfanin samar da hasken wutar lantarki.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.