BBC navigation

Kotun Argentina na sauraron shara'a mafi girma

An sabunta: 29 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:35 GMT

Zauren kotun wadda ke birnin Buenos Aires

Wata babbar kotun tarayya a kasar Argentina ta fara sauraron kara a mafi girman shariar manyan laifukan da aka tafka a lokacin mulkin soja tsakanin shekarun 1976 da 1983.

Mutane 68 ne ke fuskantar daruruwan tuhumce-tuhumcen da suka danganci satar mutane da azabtarwa da kuma kisan wadanda galibi masu neman kawo sauyi ne da ke adawa da gwamnatin mulkin soji ta wancan lokacin.

Daga cikin wadanda za su fuskanci tuhumar har da Alfredo Astiz mutumin da akewa lakabi da 'mala'ikan mutuwa', wanda tuni dama yake zaman daurin rai-da-rai a gidan yari bisa laifukan cin zarafin jama'a da ya aikata a wani sansanin tsare mutane da ya yi kaurin suna a babban birnin kasar Buenos Aires .

Masu rajin kare hakkin dan'adam sun yi kiyasin cewa sama da mutane 30,000 ne aka hallaka a lokacin, abin da aka kira 'kazamin yaki'.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.