BBC navigation

Masu zanga-zanga a Masar na kara kaimi

An sabunta: 28 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 11:26 GMT
'Masu zanga-zanga na gudu bayan jefa barkonon tsohuwa

'Masu zanga-zanga na gudu bayan an jefa hayaki musu hayaki mai sa hawaye

'Yan sanda a kasar Masar sun harba barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zanga a dandalin Tahrir, wadanda ke ci gaba da bujerewa sabuwar dokar da shugaba Morsi ya kafa.

Hakan ya biyo bayan shafe daren ranar Talata da dubban 'yan kasar suka yi a dandalin, domin nuna bacin ransu a kan dokar da Shugaban kasar na jam'iyyar 'yan uwa musulmi, Muhammad Morsi ya dauka, na baiwa kansa karfin iko mara iyaka.

Hotunan gidan Talabijin din kasar sun nuna masu zanga-zangar da suka rufe hancinsu da kyalle na wurga gwangwanin hayakin mai sa hawaye ga 'yan sandan.

A ranar Talata ne dubban masu zanga - zanga suka yi ta kwarara zuwa dandalin, suna gangami daban-daban, inda suke rera wakokin kin jinin Shugaban kasar da jam'iyyarsa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.