BBC navigation

Kotu ta yi watsi da kara a kan rarar man fetur

An sabunta: 29 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:30 GMT
Ibrahim Badamasi Babangida

Tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida

Wata babbar kotu a Nigeriya tayi watsi da karar da kungiyar kare hakkin bil adama ta SERAP ta shigar a gabanta game da wani rahoto da yayi zargin cewa an yi sama da fadi da raran kudaden da kasar ta samu a lokacin da farashin mai ya tashi tsakanin shekarar 1988 zuwa shekarar 1994 .

Kungiyar dai ta nemi kotun a kan ta umurci gwamnatin kasar ta samarwa jama'a a kasar da bayanai game da yadda aka kashe kudade da adadinsu ya zarta dala biliyan goma sha biyu.

Sai dai kotun ta ce kungiyar ta SERAP bata da hurumin yin haka ko da yake kungiyar ta ce zata daukaka karar.

Batun rarar kudaden mai dai ya faru ne lokacin mulkin tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.