BBC navigation

Sojoji sun gano makamai a birnin Zariya

An sabunta: 30 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:22 GMT
najeriya makamai

Wasu sojojin wanzar da zaman lafiya

Rundunar Soji a Najeriya ta bayyana cewa za ta yi dukkan yadda za ta iya domin damke wadanda suka kaddamar da hare haren nan guda biyu na kunar bakin wake a barikin soji da ke Jaji a jahar Kaduna ranar lahadin da ta gabata.

A wani taron manema labarai da runduna ta daya ta sojojin Najeriya da ke Kaduna ta kira ta bayyana gano wani gida a Jushin Ciki da ke birnin Zaria, inda ta ce ta sami nasarar cafke wasu muggan makamai da bama bamai a gidan bayan samun bayanai daga al'umma.

Rundunar dai ta ce wannan gida ba zai rasa nasaba da harin da aka kaddamar a Jajin ba,inda wasu motoci shake da boma boma suka kaddamar suka tarwatse a wani Chochi da ke cikin barikin na Jaji.

Jihar Kaduna ta kasashence daya daga cikin jihohin kasar dake fama da tashe tashen hankula.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.