BBC navigation

Majalisar dokokin Masar ta amince da sabon daftarin tsarin mulki

An sabunta: 30 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:49 GMT

Zauren Majalisar dokokin Masar

Majalisar dokokin da 'yan jam'iyyar 'yan uwa musulmi ke jagoranta a Masar ta rattaba hannu kan daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Bayan wani dogon zama da aka kammala da sanyin safiyar Juma'a, majalisar ta jefa kuri'ar amincewa da dukkanin tanade-tanaden daftarin 234; ciki har da wani sashe da ya tabbatarda shari'ar musulunci a zaman babban tushen dokokin kasar.

Yanzu za a aike da daftarin zuwa ga Shugaban kasar Muhammed Morsi wanda ake sa ran ya kira wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan batun, domin ya sanya hannu.

Shugaban Morsi ya ce da zarar al'ummar kasar suka amince da sabon kundin tsarin mulkin, zai dakatar da dokar da ya kafa da ta bashi karfin iko maras iyaka; wadda ta jawo gagarumar zanga-zanga a kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.