BBC navigation

Ana samun nasara wurin yaki da HIV

An sabunta: 30 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:53 GMT
Ana samun nasara wurin yaki da HIV

Kimanin mutane miliyan 34 ne ke fama da cutar HIV a duniya

A daidai lokacin da duniya ke bikin ranar AIDS ko CIDA, alkaluman baya-bayan nan na Majalisar Dinkin Duniya, sun nuna an samu raguwar yaduwar cutar da kashi 50 cikin dari a kasashe 25.

Sai dai bayanan sun sha bamban daga nahiya zuwa nahiya.

Har yanzu yankin Afrika kudu da sahara ne ya fi fama da matsalar cutar, duk da cewa wasu kasashe a yankin sun yi kokari wurin rage yaduwarta.

Babban daraktan hukumar kula da cutar na Majalisar Dinkin Duniya, UNAids, Michel Sidibe, ya shaida wa BBC cewa: "Ethiopia, Malawi da Botswana sun rage kaifin yaduwar cutar sosai, abinda ke nuna cewa za su iya shawo kanta."

'ARV' na rage yaduwar AIDS - MDD

A nahiyar Afrika, cutar AIDS ko CIDA mai karya garkuwar dan adam na ci gaba da kashe akalla mutane miliyan daya a kowacce shekara. Sai dai bayanai sun nuna cewa magungunan rage radadin cutar 'Antiretroviral', na hana ci gaba da yada cutar.

Kallimp4

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Sai dai sabbin alkaluman da aka fito da su sun nuna cewa adadin na karuwa a wasu sassan duniya, musamman tsakanin matasa, "da kuma maza 'yan luwadi".

Hukumar yaki da cutar a Burtaniya, ta ce adadin 'yan luwadi da madugon da ke kamuwa da cutar ya karu matuka a shekara ta 2011.

Haka lamarin ya ke a Amurka, inda matasa da 'yan luwadi ke kara kamuwa da cutar.

Gwamnatin Rasha ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar a watanni shidan bana ya karu da kashi 12 cikin dari idan aka kwatanta da bara.

Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin China Xinhua, ya ce sabbin wadanda ke kamuwa da cutar a kasar ya karu da kashi 13 cikin dari daga watan Janairun 2011 zuwa Oktoban shekarar.

Kasar na da kimanin mutane 500,000 da ke fama da cutar, ciki harda 70,000 da suka kamu da ita bara.

Sabbin alkaluman da hukumar UNAids ta fitar, sun nuna cewa kimanin mutane miliyan 34 ne ke fama da cutar HIV a duniya.

Yawancin mutanen dai na samun magungunan da ke rage kaifin cutar. Sai dai har yanzu akwai kimanin mutane miliyan 7 da har yanzu basa samun maganin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.