BBC navigation

Bayanai kan kisan fursunoni a Kenya

An sabunta: 30 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:57 GMT

Wasu 'yan kasar Kenya suna marhabin da hukumcin wata kotu kan cin zarafinsu yayin tawayen na Mau Mau

Wasu takardun gwamnnati da aka fitar a Birtaniya sun bayar da cikakken bayani game da kisan da aka yiwa tarin fursunoni a lokacin tawayen Mau Mau a kasar Kenya.

Fursunoni 11 ne gandurobobi suka kashe ta hanyar duka a sansanin gwale-gwale na Hola a shekarar 1959 wasu da dama kuma aka jikkata su.

Wani daga cikin fursunonin da suka tsira a lokacin na daga cikin wasu tsofaffin 'yan kenya su 3 da suke karar gwamnatin Birtaniya kan zargin gana musu azaba.

Takardun sun bada bayanin wani zaman taro da Gwamnar Kenya a lokacin mulkin mallaka Evelyn Baring ta shugabanta, wanda ya gano cewa manyan jami'an gidan yari sun nuna rashin sanin makamar aiki wajen gudanar da aikinsu amma kuma ba a gurfanar da su gaban sharia ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.