BBC navigation

MASSOB ta shigar da kara kan sojan Najeriya

An sabunta: 30 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:22 GMT

Wasu 'yan kungiyar Massob lokacin jana'izar Chief Odumegwu Ojukwu

kungiyar nan mai fafutukar tabbatar da kafuwar jamhuriyyar Biafra a yankin kudu maso gabashin Najeriya wato MASSOB, ta kai karar hukumomin soja da na ’yan sandan Najeriyar a gaban kotu.

Kungiyar na neman hukumomin su biya ta diyyar kudi naira miliyan 225, sakamakon cin zarafi da nakasa wani jami’inta da take zargin wasu sojoji da ’yan sanda sun yi abin da ta ce ya kai shi ga rasa idonsa daya.

Kungiyar ta MASSOB ta shigar da karar ce a wata babbar kotu da ke jihar Anambra, matakin da masu lura da al’amura ke ganin ya sha bamban da manufar kungiyar ta neman kafa wata kasar kanta.

Sai dai Wakilin BBC a Enugu ya ce har yanzu sammacin wannan karar bai kai ga hukumomin tsaron Najeriyar ba ko da yake ana kokarin aiwatarda hakan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.