BBC navigation

An baiwa yankin Falasdinu sabon matsayi

An sabunta: 30 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 04:56 GMT

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya mike tsaye yana tafi bayan fitarda sakamakon kuri'ar.

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar amincewa da baiwa yankin Falasdinawa matsayin kasa 'yar kallo a majalisar da gagarumin rinjaye.

Wakilan Kasashe 138 ne suka jefa kui'ar goyon baya daga cikin na kasashe 193 dake zauren,yayinda 9 suka nuna adawa, 41 kuma suka ki daukar kowane bangare.

Isra'ila da Amurka dai sun nuna kakkausar adawa da kada kuri'a amincewar.

Kuri'ar ta Majalisar Dinkin Duniya a kaikaice ta amince ne da kafuwar kasar Falasdinu tare da bata damar zama wakiliyar a hukumomi kamar su Kotun Hukumta Manyan Laifukka ta Duniya (ICC).

Isra'ila tare da Amurka na fargabar hakan zai kai Falasdinawa shigar da kara kanta bisa aikata laifukan yaki ko kuma fadada matsugunan yahudawa a Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Martani

Farayin Ministan Isra'ila Benyamin Natanyahu ya kira kuri'ar 'maras ma'ana' kuma yanzu masu lura da al'amurra za su sanya ido su ga irin martaninda kasar sa zata mayar a hukumance.

Sai dai martanin da jama'a suka mayar a gabar yammacin kogin jordan mai kayatarwa ne.

Mutane sun yi cincirindo a Ramallah suna shawagi da tutoci, suna harba bindigogi a sama, suna kuma kabbara.

Falasdinawan dai sun yi imanin cewar samun matsayin kasa 'yar kallo a Majalisar Dinkin Duniya zai kai su ga mataki na gaba a kokarin samun kasar su ta kansu, kuma ya kawo karshen fadansu da Isra'ila.

.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.