An yi ba ta kashi a kasar Masar

Zanga zanga ta yi muni a Masar
Image caption Zanga zanga ta yi muni a Masar

Fada ya barke a birnin Iskandariyya na kasar Masar tsakanin magoya baya da masu adawa da shugaba Muhammad Morsi, a daidai lokacin da ake shirin fara zaben raba-gardama kan sabon daftarin tsarin mulkin kasar.

Rahotanni sun ce an kuna motoci akan tituna.

A birnin Iskandariyyar da kuma birnin Alkahira, magoya bayan bangarorin biyu na gudanar da gangamin karshe kafin zaben da za a fara ranar Asabar.

An girke sojoji dubu 120 domin kare mazabun da ke fadin kasar.