Mandela na samun sauki a asubiti

Nelson Mandela
Image caption Nelson Mandela

Gwamnmatin Afirka ta Kudu tace tsohon shugaban Kasa, Nelson Mandela yayi fama da wata cutar huhun da yake yawan fama da ita, kuma yana samun sauki.

Mr Mandela mai shekaru 94 a duniya ya kasance a wani asibiti a Pretoria tun ranar asabar.

Wannan ne dai wani kwakkwaran bayani game da yanayin da Shugaban wanda ya yaki wariyar launin fata da ake karramawa.

An yi wa Mr Mandela maganin wata cutar lunfashi shekaru 2 da suka wuce.