Goodluck ya nemi karin kudi

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya nemi majalisar dokoki da ta duba yiwuwar amincewa da karin Naira fiye da miliyan dubu dari da sittin a kan kasafin kudin kasar na wannan shekara da ke dab da karewa.

Za a ciki wani gibi ne a tallafin mai.

Shugaban kasar dai ya ce abin da aka kebe tun da farko ya gaza, saboda haka akwai bukatar a cike gibin.

Hakan ne, a cewarsa, zai sa a kauce wa matsalar karancin mai, musamman ma a wannan lokaci da ake tunkarar bukukuwan Kirsimati.

Tuni dai wasu 'yan Najeriya suka fara nuna shakku game da hanzarin da gwamnatin ta kawo, sakamakon cuwa-cuwar da aka bankado a harkar bada tallafin mai a kasar.