Obama zai goyi bayan hana manyan bindigogi

Wani mai sayar da bindigogi a Amurka
Image caption Wani mai sayar da bindigogi a Amurka

Fadar gwamnatin Amurka White House ta ce, shugaba Obama zai goyi bayan kudurin hana mallakar manyan bindigogi bayan wani dan bidiga ya kashe mutane 26.

Daga cikin mutanen akwai yara 20 a jihar Connecticut.

Mai magana da yawun fadar Jay Carney, ya ce shugaba Obama zai goyi bayan kudurin da wani dan Majalisar jam'iyyar Democratic Senator Dianne Fienstein zai gabatar.

Kudurin zai nemi hana mallakar makamai a Amurka.

A yau dai za a ci gaba da jana'izar wandanda aka kashe.

Karin bayani