An yi harbi a wata makarantar Amurka

Wata uwa na neman bayani kan harbin da aka yi a Amurka
Image caption Wata uwa na neman bayani kan harbin da aka yi a Amurka

A wani abunda zai iya zama daya daga cikin kashe kashen jama'a da yawa a tarihin Amurka na baya bayan nan, wani dan bindiga ya harbe yan makaranta da kuma malamai a makarantar Furamare a arewa maso gabacin Jihar Connecticut.

Rahotanni sun ce dan bindiga ya fara kashe mahaifansa guda biyu, sannan ya tafi ya bude wuta kan malamai da daliban wata makarantar Firamare.

Babu dai wata sanarwa ta hukuma, amma kafofin watsa labarai na yankin sunce mutane kusan 27 ne aka kashe galibinsu kananan yara.

Jami'ai sunce dan bindigar ya mutu.

An yi amannar ya bude wuta da farko a ofishin makarantar, sannan rahotanni sun yi maganar yin harbi a akalla aji daya daga cikin azuzuwan makarantar daga bisani.

Lamarin ya faru ne a makarantar Sandy Hook, da ke a wani karamin gari na Newtown.

Dalibanta yara ne masu shekaru tsakanin biyar zuwa goma.