BBC navigation

Gina sababbin matsugunai: Amurka ta soki Isra'ila

An sabunta: 1 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 07:56 GMT

Hilary Clinton da Farayin Ministan Isra'ila Benjamin Natanyahu

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta soki shawarar da kasar Isra'ila ta yanke ta giggina matsugunan yahudawa dubu ukku Gabascin Birnin Kudus da kuma Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Da take zantawa da manyan jami'an gwamnatin Isra'ila a birnin washinton, Mrs Clinton tace daukar matakin cibaya ne ga yunkurin samun zaman lafiya.

Sai dai kuma a cewar ta kuri'ar da aka jefa a Majalisar Dinkin Duniyar ranar Alhamis ba za ta kawo Falasdinawan kusa ga samun kasar su ba, kuma za ta iya kawo sabbin kalubalai ga Majalisar da kuma Isra'ila.

Gwamnatin Obama dai na neman Isra'ila da Falasdinawa da su koma tattunawar kawo zaman lafiya ta kai tsaye, ko da yake bangarorin biyu da kuma yawancin kasashen duniya sun yi biris da kokarin shiga gaba da Amurkar keyi a wannan karon wajen samarda zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

Gwamnatin Obama dai kusan bata da wani cigaba da zata nuna ta samu a cikin shakaru hudun da suka gabata,ta fuskar shiga tsakani wajen sasanta rikicin, kasancewar wani tsarin kawo zaman lafiya na shekaru biyu da ta fito da shi a shekara ta 2010 ba je ko'ina ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.