BBC navigation

Magoya bayan Shugaba Morsi na gudanar da zanga zanga

An sabunta: 1 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 15:43 GMT
Zanga zangar magoya bayan Shugaba Morsi na Masar

Ikon da Shugaba Morsi ya baiwa kansa ya tada ƙura

Magoya bayan Shugaba Mohammed Morsi na ƙasar Masar da kuma ƙungiyar 'yan uwa musulmi ta muslim brotherhood, sun soma zanga zanga a ɗaukacin kasar a yau

Su na zanga zangar ne domin maida martani ga gangamin da 'yan adawa su kai a 'yan kwanakin nan

Zanga zangar kwanakin bayan dai ta ɓarke ne sakamakon ikon da Shugaba Morsi ya baiwa kansa da kuma yadda majalisar dake rubuta tsarin mulkin ƙasar da masu kaifin kishin Islama su ka fi rinjaye ta gaggauta kammala daftarin tsarin mulkin ƙasar

A yau ne dai Mista Morsi zai karɓi daftarin tsarin mulkin, wanda kuma ake tsammanin zai sanya wa hannu, sannan a gudanar da ƙuri'ar raba gardama akai

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.