BBC navigation

'Yan tawayen M23 sun fice daga Goma

An sabunta: 2 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 06:27 GMT

'Yan tawayen M23

Majalisar Dinkin Duniya ta ba da tabbacin cewar 'yan tawaye na kungiyar M23 a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun fice daga birnin Goma bayan mamayar shi tsawon kimanin makonni biyu.

Wani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar wannan somin-tabi ne, yana cewar har yanzu ana cikin wani hali na zaman zullumi a yankin.

'Yan tawayen sun fice ne bayan wani taro na Shugabannin yankin da aka gudanar da nufin lalubo hanyar maganin rikicin.

Tun farko dai Majaisar Dinkin Duniya ta yi umarnin a garkamawa wasu Kwamandoji biyu na 'yan tawayen takunkumi bisa zarginsu da laifin jefa kananan yara aikin soji tare da kashe wadanda suka ki amincewa su shiga aikin sojin.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.