BBC navigation

Kungiyar Alkalai a Masar ta kauracewa zabe

An sabunta: 3 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 07:51 GMT

Kotun Kolin Masar

Kungiyar dake wakiltar alkalai a kasar Masar, ta ba da sanarwa cewa 'ya'yan kungiyar ba za su sa ido ba kan Kuri'ar raba gardamar ba wanda da aka shirya gudanarwa a cikin makonni biyu masu zuwa.

Sanarwar da Kungiyar alkalan ta bayar ta biyo bayan fito-na-fito ne da ake yi tsakanin babbar Kotun Masar da 'yan jam'iyyar 'yan uwa musulmi dake goyon bayan Shugaba Mohammed Morsi.

Shugaban Kungiyar Alkalan na Masar Ahmed al-Zend shi ne ya ba da sanarwar inda ya ce, "sun yanke shawarar kauracewa sa ido a kan zaben raba gardamar da aka shirya yi ranar 15 ga watan Disamba."

Kotun tsarin mulkin kasar ta ba da sanarwa cewa za ta dakatar da aikin ta har sai illa Masha-Allahu, bayan an hana 'ya'yan ta yanke hukunci a kan halaccin majalisar da 'yan jam'iyyar 'yan uwa musulmi suka mamaye wadda ta tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.