Tarihin shugaba Dramani Mahama

John Dramani Mahama
Image caption John Mahama ya hau mulki ne bayan rasuwar shugaba Atta Mills

An haifi John Dramani Mahama ne a garin Bole-Bamboi, da ke arewacin Ghana ranar 29 Nuwamban shekarar 1958.

Ya shafe akasarin rayuwarsa daga lokacin da ya kai shekaru ashirin zuwa talatin yana karatu, a kasashe daban-daban ciki harda birnin Moscow; kana ya yi aiki na tsawon shekaru hudu a matsayin jami'in yada labarai a ofishin jakadancin Japan da ke birnin Accra.

A shekarar 1995, Mr Mahama ya yi aiki da wata kungiya mai zaman kanta mai suna PLAN International, a matsayin jami'in da ke lura da fannin daukar nauyin karatun mutane da kuma tallafa musu a kasar ta Ghana.

A watan Disambar shekar 1996, an zabi Mr Mahama a matsayin dan majalisar dokokin kasar a karon farko, kuma ya yi takara ne a karkashin jam'iyyar National Democratic Congress (NDC).

Ya zama mataimakin ministan harkokin sadarwar kasar daga watan Afrilu na shekarar 1997 zuwa watan Nuwamban shekarar 1998; sannan ya zama ministan ma'aikatar shekaru biyu bayan hakan.

A lokacin da Mr Mahama ke ministan harkokin sadarwar, ya kuma yi aiki a matsayin shugaban hukumar sadarwar kasar, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta fannin sadarwar kasar, bayan an cire tallafin sayar da ma'aikatar ga kamfanoni masu zaman kan su a shekarar 1997.

Mr Mahama ya zama mamba a kungiyar 'yan majalisun dokokin kasashen Afirka wacce ke da mazauni a birnin Pretoria, na kasar Afirka ta Kudu daga shekarar 2004 zuwa 2011 - shi ne ma shugaban rukunin 'yan majalisun kasashen Afirka ta yamma a kungiyar.

A ranar bakwai ga watan Janairun shekarar 2009, Mr Mahama ya zama mataimakin shugaban kasar Ghana, sannan ya zama shugaban kasar ranar 24 ga watan Yulin shekarar 2012 bayan rasuwar shugaban kasar John Atta Mills.

Yana auren Lordina Mahama kuma suna da 'ya'ya bakwai.

Ana kalllon John Dramani Mahama, a matsayin mutumin da ke fafutikar kwato 'yancin marasa galihu.

Haka kuma mutum ne da ke da sha'awar kare muhalli, musamman yadda yake yaki da matsalolin gurbacewar muhalli, da aikin sarrafa robobi ke haifarwa a kasashen Afirka.

Mahama Kirista ne da ya yi fice a fannin tarihi, da rubuce-rubuce, da harkokin sadarwa.

A kwanakin baya ne ya rubuta wani littafi mai suna "My First Coup d'Etat", a turance, inda ya yi nazari kan matsalolin siyasar da suka yi wa kasashen Afirka dabaibayi tun samun 'yancin kan su.

Karin bayani