Zanga-zanga kan sakin aure a Indonesia

Aceng Fikri
Image caption Aceng Fikri shugaban Gundumar Garut a Java ta Yamma

Dubban dalibai ne da sauran masu fafutuka suka yi zanga-zanga kan wani zababben shugaban gunduma a Indonesia wanda ya saki matarsa mai shekaru goma sha wani abu da haihuwa, ta hanyar aika ma ta da sakon wayar salula, kwanaki hudu bayan daura auren nasu.

Aceng Fikri, wanda aka zaba shugaban Gundumar Garut, a Java ta Yamma, ya fito bainar jama'a ya nemi afuwa bisa korafin da ake yi.

Mr Fikri, dan shekaru 40, yana da aure da 'ya'ya uku, kafin ya auri yarinyar 'yar shekara 17 a matsayin mata ta biyu.

Masu zanga-zangar na kira ne ga shugaban gundumar ta Garut, a Java ta Yamma, da ya sauka daga kan mukaminsa.

Aceng Fikri ya saki yarinyar ce wacce ya aura a matsayin matarsa ta biyu, bisa tsari na addinin Musulunci.

An ce ya sake ta ne bayan da bai same ta a matsayin budurwa ba.

Masu aiko da rahotanni sun ce babu alamar cewa 'yan sanda za su tuhume shi.

Sai dai shugaban kasar Indonisea Susilo Bambang Yudhoyono ya umarci ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar da ta gudanar da bincike kan lamarin.