Nakassu suna bukatar a kare hakkokinsu

Nakasassu suna zanga-zanga

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware dan bikin ranar mutane masu buk’ata ta musamman ta duniya da ake yi shekara shekara.

Tun a shekarar 1976 majalisar ta ayyana 1981 a matsayin shekarar mutane masu bukata ta musamman, inda kuma aka fara bikin ranar daga 3 ga watan Disamba 1992.

Manufar ware ranar ita ce fadakar da al’umma batutuwa da suka shafi nakasa, da k’ok’arin bayyana irin hakkokin da nak’asassu suke da su.

An kuma yi batun alfanun da za a iya samu idan aka shigar da mutanen da ke da ‘ cikin dukkan al'amura na rayuwa da suka had’a da siyasa da tattalin arziki da kuma zamanakewa.

Taken bikin na bana dai shi ne, Kawar da Duk Wasu Bambance-bambance don Samar da Daidaito Tsakanin Jama’a.

Nak’asassun dai suna gamuwa da k’alubale daban-daban a ko’ina a duk fadin duniya.