Birtaniya da Faransa sun ja kunnen Isra'ila

Ana ci gaba da matsin lambar diplomasiyya kan Isra'ila domin ta sake nazari kan shirinta na gina wasu sabbin gidajen Yahudawa a yankunan Palasdinawa da take mamaye da su.

Birtaniya da Faransa duk sun kira jakadunsu a Isra'ila domin su bayyana rashin jin dadinsu kan shirin, wanda aka bayyana shi a matsayin martani ga kuri'ar da aka kada a majalisar dinkin duniya wadda ta amince a baiwa Palasdinawa karin matsayi.

Birtaniya ta ce gina matsugunan Yahudawan zai yi barazana ga yuwuwar cinma yarjejeniya kan kafa kasashe biyu, kuma za a dauki mataki mai karfi kan Isra'ilar, idan ta ci gaba da wannan aiki.

A makon da ya gabata ne ministan harkokin wajen Birtaniya William Hague ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa shekarar 2013 nada matukar muhimmanci a shirin tattaunawar sulhu tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Muddin Isra'ila ta aiwatar da shirinta na gina sabbin rukunin gidaje dubu uku a yamma da Kogin Jordan tare da raba Falasdinu da kasarta, to ko shakka babu ba inda shirin sulhun zai je.

A yau gwamnatocin Birtaniya da Faransa na kokarin aiwatar da wani yunkuri na dakatar da shirin Isra'ila na gina gidajen.

Ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya ta ce ta yi sammacin Jakadan Isra'ila a Birtaniyar, Daniel Taub domin nuna kin amincewarta da shawarar Isra'ila na fadada matsugunnan yahudawa a yankunan Falasdinawa.