Ghana na fama da karancin wutar lantarki

Turakan wutar lantarki
Image caption Turakan wutar lantarki

A watannin baya-bayan nan kasar Ghana ta jima tana fuskantar matsalar karancin wutar lantariki.

Hakan ya sa yanzu kamfanin samar da wutar lantarkin kasar yake tsimin wutar lantarikin ta hanyar raba wutar daga wannan sashe zuwa wancan.

A kan dauke wutar na tsawon sa'oi don baiwa wani sashe.

Lamarin da mutanen kasar suka ce na tasirin a kan rayuwarsu da ayyukansu na yau da kullum.

Hakan kuma na aukuwa ne a yayin da gwamnatin NDC ta ce tana zawarcin masu saka jari, don su zo su saka jari cikin kasar.