Ƙungiyar tsaro ta NATO ta gargaɗi Syria

Anders Fogh Rasmussen
Image caption NATO ta yiwa Syria gargaɗi

Shugaban Ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO ya ce idan Syria ta kuskura ta yi amfani da makamai masu guba, to kuwa ƙasashen duniya ba zasu yi wata wata ba zasu ɗauki mataki a kanta.

Shugaban ya ce, amfani da makamai masu guba, abu ne da ƙasashen duniya ba zasu amince da shi ba.

Wannan gargaɗi daga Anders Fogh Rasmussen ya biyo bayan wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba dake cewa akwai yuwuwar gwamnatin Syria na tana tunanin amfani da irin waɗannan makamai yayinda ake ci gaba da yaƙin basasa a ƙasar.

Mista Rasmussen ya bayyana haka ne a wani taron ƙungiyar ta NATO wanda ake sa ran zai amince da buƙatar da Turkiyya ta gabatar na a girke ma ta makaman Patriot masu bada kariya daga harin makamai masu linzami, domin tunkarar dukkanin wata barazana daga tsallaken iyakarta da Syria.

Karin bayani